Isa ga babban shafi
Najeriya

'Likitoci sun gamsu da aikin da suka yi ma Yusuf Buhari'

Fadar shugaban Najeriya ta musanta rahoton da ke cewa an fitar da ɗan shugaban ƙasar, Yusuf Buhari zuwa ƙasar waje domin duba lafiyarsa bayan raunin da ya samu sakamakon hatsarin babur.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da dansa Yusuf Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da dansa Yusuf Buhari. Pulse.ng
Talla

Kakakin fadar Shugaban ƙasar Najeriya Garba Shehu wanda ya tabbatar da hatsarin da Yusuf Buhari ya yi, ya ce yanzu haka ɗan shugaban ƙasar na kwance a asibiti inda iyalinsa ke tare da shi.

Ya ƙara da cewa likitoci sun gamsu da aikin da suka yi wa Yusuf ɗin a kansa da kuma ɗorin da aka yi masa a ƙafar da ta karye.

Garba ya ce likitoci na ba shi kulawar da ta dace, sannan su ne kaɗai, da kuma iyayensa za su iya tantance ko za a fitar da ɗan shugaban zuwa ƙasar waje ko kuma a'a.

A ranar Laraba ne Yusuf Buhari ya samu karaya a ƙafarsa, tare da buguwa a kansa sakamakon hatsarin babur da ya samu a unguwar Gwarimpa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.