Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bai wa Sifeto Janar na 'yan sanda umarnin komawa Benue

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bai wa Sifeto Janar na ‘yan sandan kasar Ibrahim Idris umarnin komawa jihar Benue, domin kawo karshen rikicin da ya barke tsakanin manoma da makiyaya.

Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris.
Sifeto Janar na 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris. Daily Post
Talla

Umarnin ya zo ne cikin daren ranar Litinin, yayin da aka sake samun rahoton hallaka wasu mutane a kananan hukumomin Guma da Logo a jihar ta Benue.

A ranar Litinin ministan cikin gida na tarayyar Najeriya AbdulRahman Dambazau, ya jagoranci taron da ya hada gwamnonin jihohi 6 da ke fama da rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, da kuma inda ake yawan satar jama’a, a wani yunkuri na samar da zaman zaman lafiya a wadannan jihohi.

Jihohin da lamarin ya shafa kuwa su ne Taraba, Benue, Adamawa, Nasarawa, Niger da kuma Kaduna.

Taron ya amince da samar da akalla filin kiwo da fadinsa ya kai kadada dubu biyar a sassan kasar, domin ingantawa tare da zamanantar da sha’anin kiwo, a matsayin wata hanyar magance yawaitar samun rikici tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya.

Ministan cikin gidan kasar Abdurrahman Bello Dambazau ya yi wa wakilinmu Aminu Ahmed Manu karin bayanai dangane da matakan da suke shirin dauka.

00:51

Minsitan cikin gidan Najeriya AbduRahman Bello Dambazau kan taron inganta sha'anin tsaro a jihohi 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.