Fadar gwamnati ta musunta rade-rade kan takarar Buhari
Fadar gwamnatin Najeriya ta musanta rahotanni da ke cewa shugaba Muhammadu Buhari ba shi da tabbacin sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a shekarar 2019.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sanarwar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin yiwuwar sake takarar shugaban a zaben shekara mai zuwa.
A baya-bayanan ministan sadarwa kasar Adebayo Shittu wanda ya bada gudunmawa wajen nasaran zaben Buhari a zaben 2015 ya ce, zai jagoranci kungiyar magoya bayan Buhari don yi ma sa yakin neman zabe.
Ana saran gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabairun 2019, yayin da jam'iyyun siyasa za su gabatar da ‘yan takaransu daga ranar 18 ga watan agusta zuwa 7 ga watan Oktoba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu