Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe ƴan-sanda 7 da sojoji 2 a Numan

Kwamandan sojin Najeriya da ke kula da runduna ta 23 a Yola da ke arewacin ƙasar, Birgediya-Janar Bello Muhammed, ya ce ƴan-sanda 7 da sojoji 2 aka kashe a rikicin da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a ƙaramar hukumar Numan.

'Yansandan Najeriya.
'Yansandan Najeriya. Reuters
Talla

Yayin da yake jawabi ga mutanen yankin, Janar Muhammed ya yi gargaɗin cewa rundunarsa da sauran jami’an tsaro za su murƙushe duk wasu mutane da suka ci gaba da haifar da tashin hankali a yankin.

Jami’in ya ce rikicin da aka fara a Numan ya yaɗu zuwa wasu ƙananan hukumomin da ke jihar, irin su Girei, da Demsa, da kuma Lamurde, inda daga bisani ya yaɗu zuwa jihar Taraba da ke makwaftaka.

Janar Muhammed ya koka kan rawar da sarakunan gargajiya da ƴan-siyasa ke takawa wajen tunzura rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.