Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari zai jagoranci taro da tsaffin shugabannin Najeriya

A yau Alhamis, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai jagoranci wani taron na musamman na Majalisar Koli ta kasar a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS
Talla

Karo na uku kenan da Buhari zai jagoranci irin taron, wanda tsaffin shugabannin Najeriya da ke raye suka halarta.

Daga cikin tsaffin shugabannin da ake sa ran zasu halarci taron akwai, Shehu Shagari, Olusegun Obasanjo, da kuma Goodluck Jonathan.

Sauran tsaffin shugabannin Najeriyar sun hada da, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, Janar Ibrahim Babangida, Janar Abdulsalami Abubakar, da kuma Chief Ernest Shonekan.

Daga cikin batutuwan da ake sa ran taron zai tattauna a kai, akwai hare-haren da ake zargin makiyaya da kai wa sassan Najeriya, da sauran hasarar rayukan da suka auku a sassan kasar, da kuma sauran batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.