Isa ga babban shafi
Najeriya

Janye sojoji ne ya bada damar sace daliban Dapchi - Gaidam

Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam ya dora alhakin sace daliban makarantar ‘yan mata ta Dapchi da ake zargin mayakan Boko Haram da yi, akan janye jami’an sojojin da ke bai wa yankin tsaro a baya.

Harabar makarantar 'yan mata ta Dapchi da ke jihar Yobe da mayakan da ake zargin na Boko Haram ne suka sace dalibanta a arewa maso gabashin Najeriya.
Harabar makarantar 'yan mata ta Dapchi da ke jihar Yobe da mayakan da ake zargin na Boko Haram ne suka sace dalibanta a arewa maso gabashin Najeriya. REUTERS/Ola Lanre
Talla

Gaidam ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce kwanaki kalilan kafin aukuwar harin aka janye baki dayan shingayen binciken sojoji daga garin na Dapchi, da sauran yankunan da ke kusa, abinda ya bai wa maharan damar aiwatar da mugun nufin su na sacen daliban.

Sai dai Gaidam ya sha alwashin gwamnati ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an ceto daliban da kuma sada su da iyalansu.

Gwamnan na Yobe, ya bukaci rundunar sojin Najeriya da ta mayar da jami’anta zuwa sassan jihar da ta janye domin ci gaba da samar da cikakken tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.