Isa ga babban shafi

Rundunar 'yan sandan Zamfara ta dakile yunkurin kai hari a Anka

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sanar da dakile yunkurin wasu gungun ‘yan bindiga na kai hari kan yankin Wuya da ke karamar hukumar Anka.

Jami'an 'Yan sandan Najeriya.
Jami'an 'Yan sandan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Muhd Shehu, wanda ya bayyana haka a garin Gusau, inda ya ce an samu musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ‘yan bindigar wadanda ke haye akan Babura, kafin su tsere zuwa cikin jeji.

Sai dai ‘yan sanda sun yi nasarar kama daya daga cikinsu, tare da kwace tarin makamai daga hannunsa.

Wani rahoto da gwamnatin jihar Zamfara ta fitar ya nuna cewa daga shekarar 2011 zuwa yanzu, ‘yan bindiga sun hallaka mutane dubu 1,321 yayin da suka jikkata wasu mutanen dubu 1,881.

Kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Alhaji Sanusi Rikiji, wanda shi ne shugaban kwamitin tance-tance barnar da ‘yan bindiga suka yi jihar ta Zamfara da kuma basu tallafi, ya ce sama da shanu dubu 10,000 barayi suka sace, yayin da suka lalata gonaki da fadinsu yakai kadada dubu 2,688, sai kuma gidaje 10,000 da ‘yan bindigar suka lalata daga shekarar ta 2011 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.