Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na gaf da kwato dukiyarta da aka boye a ketare

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabon shiri na kwace kudade da kuma kadarorin da wasu tsaffin gwamnoni, ministoci da kuma sanatocin kasar suka wawure tare boye su a kasar hadaddiyar daular Larabawa.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Ibrahim Magu.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, Ibrahim Magu. Daily Post
Talla

A daren jiya Ministan Shari’ar Najeriya Abubakar Malami da mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Ibrahim Magu, suka tashi zuwa Dubai domin kammala cike sharuddan karbe tarin dukiyar da aka yi sama da fadi da ita.

Rahotanni sun ce yawan tsaffin mukarraban gwamnatin Najeriyar da matakin ya shafa zun zarta 20. Koda yake gwamnati bata wallafa sunayen wadanda lamarin ya shafa ba, bayanai masu tushe sun nuna cewa, daga cikinsu kuma akwai tsohuwar Minstar albarkatun mai Diezani Alison-Madueke da kuma tsohuwar rusasshen bankin Oceanic Mis Cecilia Ibru.

Sauran tsaffin masu mukaman siyasar sun hada da wasu tsaffin gwamnoni akalla 9, da kuma tsaffin ministoci 6.

A ranar 19 ga watan Janairu na shekarar 2016, Najeriya ta sa hannu yarjejeniyoyi 6 tsakaninta da Hadaddiyar Daular Larabawa, a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci kasar, daga cikin yarjejeniyoyin akwai batun mikawa Najeriya kudaden da tsaffin mukarraban gwamnatin kasar suka sace, tare da boyewa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.