Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a 2019

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019 kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya rawaito.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da aniyarsa ta neman wa'adi na biyu akan karagar mulkin kasar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da aniyarsa ta neman wa'adi na biyu akan karagar mulkin kasar Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin taron shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin kasar a yau Litinin.

A karon farko kenan da shugaban ke sanar da aniyarsa karara a bainal jama’a duk da cewa a baya wasu alamomi sun nuna cewa, babu shakka shugaban na da burin neman wa’adi na biyu akan karagar mulki.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da wasu da suka hada da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ke ci gaba da caccakar salon shugabancin Buhari tare da gargadin sa da ya kauce wa sake tsayawa takara bisa zargin sa da gazawa ta fannoni da dama da suka hada da bunkasa tattalin arzikin kasar.

Sai dai wasu kuwa na yaba wa shugaban musamman kan jajircewarsa wajen yaki da ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido da tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Abubakar Atiku na daga cikin wadanda suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takara a zaben 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.