Isa ga babban shafi
Najeriya

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 3 a Masallacin garin Bama

Wasu yan kunar bakin wake  sun kashe mutane 3 a wani Masallaci a garin Bama dake Jahar Borno a Najeriya. Shidai wannan garin yanzu haka ana kan  sake gina shi bayan da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram suka kacaccala shi a  yankin Arewa maso gabashin kasar.

Kokarin agaji bayan harin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya
Kokarin agaji bayan harin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya © RFI
Talla

Wani ganau, mai suna  Baba shehu Gulumba da ke a garin  Bama ya ce maharan mace da Namiji, sun tarwatsa kansu ne a lokacin da ake sallar Asubah a garin na  Bama da ke jihar Borno.

Babban jami’in Sojin Najeriya da ke aiki a garin na Bama ya shaida wa manema labarai cewar hakika harin ya faru, kuma a lokacin, an kwashe akalla mutane 9 da suka samu raunuka  zuwa Assibiti, kuma bayanai na nuna cewar ankaisu ne zuwa Asibiti a garin Maiduguri.

Harin na zuwa ne akalla sati guda bayan da mutanen garin suka fara komawa gida sakamakon zaman lafiya da aka fara samu a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.