Isa ga babban shafi
Najeriya

An kama dan Boko Haram da ke shirya kai hare-hare a Benue

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar cafke wani dan kungiyar Boko Haram, Aminu Yaminu da ke amsa sunan Tashaku, wanda ke kyautata zaton shi ne ke shirya mafi akasarin hare-haren da ake kaiwa a jihar Benue.

Wasu jami'an sojin Najeriya.
Wasu jami'an sojin Najeriya. REUTERS/Tim Cocks
Talla

Wata runduna ta musamman da ta kunshi sojoji, ‘yan sanda da kuma jami’an farin kaya na DSS ce ta cafke Tashaku a garin Makurdi.

Rundunar sojin Najeriya ta kara da cewa, binciken sirri da aka gudanar ya nuna cewa wanda suka kama yana shirin kaddamar da wasu sabbin hare-haren ne a jihar ta Benue, tare da taimakon ‘yan uwansa da ke jihohin Bauchi, Borno, Yobe da kuma Nasarawa.

Tun daga watan Janairun da ya gabata, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka hallaka mutane 73, Jihar Benue ke fuskantar karuwar hare-haren da ake dangantawa da Fulani makiyaya, lamarin da ya yi tilastawa dubban mazauna sassan jihar da hare-haren ya shafa yin gudun hijira.

A ranar Talata da ta gabata, wasu ‘yan bindiga suka kai harin kan wani Mujami’ar darikar Katolika, a karamar hukumar Gwer, inda suka hallaka mutane 19 ciki harda manyan limaman Mujami’ar guda biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.