Isa ga babban shafi
Najeriya

Bazan taba goyon bayan sake takarar Buhari ba - Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ba zai taba goyan bayan aniyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta sake tsayawa takarar shugabancin kasar wa’adi na biyu ba.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, cikin raha tare da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, bayan kammala babban zaben Najeriya na 2015.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, cikin raha tare da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, bayan kammala babban zaben Najeriya na 2015. AFP
Talla

Obasanjo ya kara da cewa sukkanin kalaman da ya furta akan shugaba Buhari cikin wasikarsa ta ranar 23 ga watan Janairun wannan shekara inda ya shawarce shi da janye aniyar tazarce suna nan daram, bai janye su ba.

Tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana haka ne ta hannun mai nashi shawara akan kafafen yada labarai Kehinde Akinyemi, yayinda yake karyata rahotannin da ke cewa a halin yanzu ya janye adawar da yake wa shugaba Muhammadu Buhari, kuma kari kan haka yana goyon bayan sake tsayawrsa takara.

Cif Olusegun Obasanjo, ya kuma bayyana rashin gamsuwa akan ziyarar da shugaban Najeriya Buhari ya kai zuwa Amurka, wadda ya ce bata amfanawa ‘yan Najeriya komai ba, kuma koda akwai abin amfanin, bai taka kara ya karya ba.

Yayinda yake tsokaci akan kalaman na tsohon shugaban Najeriya, mai baiwa shugaba Buhari shawara akan kafafen yada labarai Femi Adeshina, ya ce, kalaman basu kai darajar wadanda za a maida wa raddi ba, domin ko kusa basu da masaniya akan rahotannin da ke cewa a halin yanzu Obasanjo ya lashe amansa na sukar gwamnatin Buhari, ballantana a ce ma daga bangarensu aka samu masu yada kalaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.