Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Najeriya ta daure tsohon gwamna shekaru 14

Babbar kotun Najeriya da ke birnin Abuja ta yanke hukuncin dauri a gidan yari kan tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame har tsawon shekaru 14 ba tare da zabin biyan tara ba.

Jolly Nyame, tsohon gwamnan Taraba
Jolly Nyame, tsohon gwamnan Taraba Premium Times
Talla

Mr. Nyame ya fuskanci wannan hukuncin ne bayan da kotun ta same shi da laifuka 27 daga cikin 41 da ake zargin sa da aikatawa da suka shafi karkatar da kudaden talakawa.

Shara’ar ta samo asali ne bayan da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin sa da karkatar da Naira biliyan 1 da miliyan 64 a lokacin da ya rike da mukamin gwamnan Taraba daga shekarar 1999 zuwa 2007.

Ko da yake an yanke wa gwamnan hukuncin daurin shekaru 14 ne saboda samun sa da laifin karkata Naira miliyan 350 a wani kamfani, Saman Global a cikin makwanni 5 a shekarar 2005, duk da dai Nyame ya ce ba shi da masaniya kan wannan kamfani da ake zance akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.