Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya sanya hannu kan dokar shekarun takara

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar rage shekarun tsayawa takarar zabe wadda za ta bai wa matasa damar shiga fagen siyasa domin damawa da su.

Lokacin da shugaba Buhari ke sa hannu kan dokar rage shekarun takara a Najeriya
Lokacin da shugaba Buhari ke sa hannu kan dokar rage shekarun takara a Najeriya RFI/Kabir Yusuf
Talla

A wani shagube da ya yi wa matasan da aka gayyata daga jihohi 36 domin halartar bikin sanya hannun, shugaba Buhari ya bukace su da su kauce wa tsayawa takarar shugaban kasa har sai bayan zaben shekara mai zuwa.

A karkashin sabuwar dokar, an rage shekarun tsayawa takarar shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 30, gwamna kuma shekaru 30 maimakon 35, yayin da masu shekaru 25 na iya tsayawa takarar Majalisar Dokokin Jihohi, kana mai shekaru 30 zai tsaya takarar Majalisar Tarayya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.