Isa ga babban shafi
Najeriya

nPDP ta musanta sa son zuciya a bukatun da ta mikawa gwamnati

Kungiyar tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP da a yanzu ke APC mai mulkin Najeriya, ta musanta mikawa gwamnati bukatar dakatar da shara’ar da ake yi wa shugaban majalisar dattijan kasar Sanata Bukola Saraki akan kin bayyana wasu kadarorinsa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara. TheCable
Talla

Shugaban kungiyar ta tsaffin ‘yan PDP da ke APC Alhaji Abubakar Baraje ne ya musanta rahoton, wanda ya bayyana shi a matsayin kage.

Da farko dai an rawaito cewa daga cikin manyan bukatun da kungiyar ta tsaffin ‘yan PDP da ke cikin APC suka mikawa gwamnatin Najeriya a taron su na ranar litinin, akwai daukar mataki akan maida magoya bayan kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso saniyar ware a tarukan jam’iyyar APC da ya gudana a kananan hukumomin Bauchi da Kano.

Sauran bukatun sun hada da neman, a daina yi wa wasu ‘yan tsaffin jami’yyar PDPn bita da kulli, da sunan binciken hukumar EFCC mai yakar cin hanci da rashawa a Najeriya, da kuma dakatar da shara’ar shugaban majalisar dattijai kan kin bayyana wasu kadarorinsa da kotu ke sauraro.

Yayinda ya ke yiwa sashin Hausa na RFI karin bayani ta wayar tarho akan musanta rahoton na baya bayan nan, kakakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Muhammad Isa, ya ce dukkanin sharuddan da kungiyar tsaffin ‘yan PDP da ke APC suka mikawa gwamnati, bukatu na jam’iyya da basu shafi mutum guda ba.

A cewar kakakin shugaban majalisar dattijan, babu gaskiya cikin rahoton da ya rawaito cewa sun sanya son zuciya a cikin muradun nasu.

01:00

Kakakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Muhammad Isa

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.