Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun tilasta wa mazauna kauyukan Zamfara gudun hijira

Rahotanni daga jihar Zamfara a tarayyar Najeriya na cewa hare-haren ‘yan bindiga ko barayin shanu na tilasta wa mazauna kauyukan jihar yin gudun hijira zuwa wasu yankunan makwabciyarsu Katsina.

Wasu daga cikin mazauna kauyukan Mada, da ke Jihar Zamfara, da suka tsere zuwa cikin gari, domin gujewa hare-haren 'yan bindiga.
Wasu daga cikin mazauna kauyukan Mada, da ke Jihar Zamfara, da suka tsere zuwa cikin gari, domin gujewa hare-haren 'yan bindiga. RFIHAUSA
Talla

Matsalar hare-haren dai na ci gaba da girmama a sassan jihar ta Zamfara, la’akari da cewa ko a baya bayanan ‘yan bindiga sama 200 ne suka kai wa akalla kauyuka 10 da ke garin Mada farmaki.

Kauyukan da hare-haren suka shafa sun hada da, Fura Girke, Majira, Kanawa, Yargeba, Ta-koka, Bargaja, Bundungel, Bantsa, Unguwar Matandada kuma Makera.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa sashen Hausa na rfi cewa, ‘yan gudun hijirar sun saka su cikin halin bukatar taimakon kayan abinci, lakari da cewa akwai mata da kananan yara masu yawa a cikinsu.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Ibrahim Wakkala, ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya da ta kai wa al’ummar jihar dauki dangane da masifar hare-haren ‘yan bindiga da ke ci gaba da kazanta a jihar.

Wakkala ya yi rokon ne jiya Juma’a, a lokacin da ya ziyarci garin Mada, inda a yanzu haka mazauna kauyukan 10 da hare-haren ‘yan bindigar su ka shafa ke gudun hijira.

Sai dai ga alama mataimakin gwamnan jihar ta Zamfara bai ji dadin ziyarar ba, kasancewar mutane a garin na Mada sun nuna matukar fusata dangane da jinkirin da ake ci gaba da samu wajen magance musu matsalar tsaron da ke damunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.