Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a soma binciken tauye hakkin dan adam a gidajen yarin 'yan sanda

Sufeto Janar na Rundunar ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya bai wa hukumar kare hakkin bil’adama ta kasar damar yin cikakken bincike a illahirin gidajen yarin kasar.

Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris.
Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris. independent.ng
Talla

Matakin na zuwa ne bayan da hukumar ta bukaci yin bincike don sanin halin da mutane ke ciki a gidajen yarin, da kuma yadda rundunar yan sanda dake yaki da masu fashi da makami da aka fi sani da SARS, ke tafiyar da ayukansu.

Comrade Ya’u Musa Sakaba, wani dan rajin kare hakkin bil’adama ne a Najeriya, yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, ya ce, a ziyarar da suka kai zuwa inda ake tsare da masu laifi, sun ga misalai na tauye hakkin dan adam.

Comrade Sakaba ya ce sau da dama idan jami’an na SARS suka kama mutanen da suke zargi, to fa ana tuhumarsu ne tamkar an kama su dumu dumu da lafin da ake zarginsu da aikatawa.

01:01

Comrade Ya’u Musa Sakaba kan soma binciken tauye hakkin dan adam a gidajen yarin 'yan sanda

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.