Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta hada gwiwa da jam'iyyu 34 domin zaben dan takara guda

Shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya da jagororin wasu jami’iyyun 34, ciki har da sabuwar jam’iyyar R-APC da ta balle daga APC, sun taru a garin Abuja kan tunkarar zaben 2019.

Wasu magoya bayan jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
Wasu magoya bayan jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya. Premium Times
Talla

Yayin taron, jam’iyyun sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar amincewa da hada kai wajen marawa dan takara guda, da zai fafata da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019.

Daga cikin jami’yyun da suka halarci wannan taro akwai, ADC, SDP, NCP da kuma jami’yyar adawa ta Labour.

A bangaren jiga-jigan ‘yan siyasar da fuskokinsu suka bayyana a taron hadin gwiwar jami’yyun adawar kuwa, daga ciki, akwai tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus, da kuma shugaban sabuwar jam’iyyar R-APC da ta balle daga jam’iyya mai mulkin Najeriya ta APC.

A makon da ya gabata ne tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP da ke APC, wato ‘yan kungiyar nPDP, sun kafa sabuwar jam'iyyar APC da suka sanya wa suna (R-APC).

Yayin sanarwar, tsaffin ‘yan jami’yyar PDP da ke APC sun bayyana Alhaji Buba Galadima a matsayin shugaban sabuwar jam’iyyar ta R-APC, Dakta Atanda a matsayin sakataren jam’iyyar, sai kuma Kazeem Afegbua a matsayin sakataren yada labaran jam'iyyar.

Yayinda ya ke yi wa manema labarai karin bayani, Alhaji Buba Galadima, ya ce tilas ce ta saka su daukar wannan mataki, la’akari da cewa jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, sun gaza sauraron kokensu na mayar da su saniyar ware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.