Isa ga babban shafi
Najeriya

Hare-haren 'yan bindiga ba zai dore ba - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan kasar da su kara hakuri dangane da matasalolin tsaron da ake fuskanta a sassa daban daban, kasancewar gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana tare da dukkanin hukumomin tsaro, domin kawo karshen ta’addancin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Dan Kitwood
Talla

Shugaba Buhari ya yi kiran ne yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da wasu ‘yan bindiga suka yi wa mutane da dama a ciki da wajen kauyen Gandi da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto, ciki har da wani Hakimi.

Cikin sakon da ya aiki ta hannun kakakinsa Garba Shehu, Shugaban Najeriyar ya bayyana mamaki da kaduwa dangane da yadda masu kisan gillar ke hallaka wadanda basu ba basu gani ba, ba tare da dalilin komai ba.

Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar cewa ta gano tushen wannan matsala ta hare-haren ‘yan bindiga musamman ma wajen gano wadanda ke tallafawa ta’addacin a boye.

A makon da ya gabata ne, yayin wata ziyara da ya kai garin Munguno a jihar Borno, shugaba Buhari ya zargi wasu gurbatattun ‘yan siyasa da haddasa matsalolin tsaro a sassan Najeriya, domin cimma manufofin siyasa, musamman shafawa gwamnatinsa bakin fenti.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.