Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta bai wa jiga jigan APC wa'adin mako 2 kan batun sauyin sheka

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta bai wa shugaban majalisar dattijan kasar Sanata Bukola Saraki tare da takwaransa na majalisar wakilan kasar, da ke sunsunarta, wa’adin makwanni biyu, su yanke shawarar komawa cikinta, ko kuma ci gaba da zama cikin jam’iyyarsu.

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki tare da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara.
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki tare da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara. NigerianEye
Talla

Sauran jiga-jigan ‘yan jam’iyyar ta APC da wa’adin na PDP ya shafa, kamar yadda jaridar the nation ta rawaito, sun hada da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulFatah Ahmed, da kuma gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, sai kuma tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Ana sa ran nan da wani gajeren lokaci, Bukola Saraki zai jagoranci taro da wasu manbobin kungiyar tsaffin ‘yan PDP da ke APC, da suka rikide zuwa R-APC, domin yanke shawarar karshe.

A farkon watan Yuni na 2018, tsaffin ‘yan jam’iyyar PDP da ke APC, wato ‘yan kungiyar nPDP, sun kafa sabuwar jam'iyyar APC da suka sanya wa suna (R-APC).

Kungiyar ta nPDP ta bayyana daukar matakin ne yayin ganawa da manema labarai otal din Sheraton da ke Abuja, a ranar 4 ga watan Yuli na shekarar 2018.

Yayin sanarwar, tsaffin ‘yan jami’yyar PDP da ke APC sun bayyana Alhaji Buba Galadima a matsayin shugaban sabuwar jam’iyyar ta R-APC, Dakta Atanda a matsayin sakataren jam’iyyar, sai kuma Kazeem Afegbua a matsayin sakataren yada labaran jam'iyyar.

Yayinda ya ke yi wa manema labarai karin bayani, Alhaji Buba Galadima, ya ce tilas ce ta saka su daukar wannan mataki, la’akari da cewa jam’iyyar APC mai mulki da kuma gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, sun gaza sauraron kokensu na mayar da su saniyar ware.

Galadima ya kara da cewa R-APC jam’iyya ce halastaciyya, wadda ba ta bukatar tunkarar hukumar zaben Najeriya domin yi mata rijista, zalika duk wanda bai gamsu da matakinsu na kafa jam’iyyar ta R-APC ba, ya na da damar garzayawa kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.