Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan kunar bakin wake sun hallaka kansu a Maiduguri

Rayukan mutane akalla biyar sun salwanta a birnin Maiduguri da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, a harin da wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai yankin Kaleri.

Wasu daga cikin jami'an agaji yayin kwashe gawarwakin 'yan kunar bakin waken da suka kai hari unguwar Kaleri da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno. 5, ga watan Agusta, 2018..
Wasu daga cikin jami'an agaji yayin kwashe gawarwakin 'yan kunar bakin waken da suka kai hari unguwar Kaleri da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno. 5, ga watan Agusta, 2018.. RFIHAUSA/Bilyaminu Yusuf
Talla

Baki dayan wadanda suka hallaka ‘yan kunar bakin waken ne guda biyar, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.

Shaidu sun ce ‘yan kunar bakin waken sun da maza biyu, da kuma ‘yanmata uku, wadanda suka yi yunkurin shiga wasu gidaje da ke gaf da kasuwar Kaleri, ta hanyar kwankwasa musu kofa tamkar wasu baki.

A cewar wani mazaunin unguwar ta Kaleri daya daga cikin masu gidajen da aka kwankwasawa yana bude kofarsa, daya daga cikin ‘yan matan ta tarwatsa bam din da ke jikinta, nan ta ke ta hallaka tare da jikkata wasu mutane 3.

Shaidar ya kara da cewa ganin abinda ya faru ga ‘yar uwarsu ne ya sa sauran ‘yan kunar bakin waken fasa bama baman da ke jikinsu, inda su kadai suka hallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.