Isa ga babban shafi
Najeriya

Ko me ya hana Majalisar Najeriya komawa bakin aiki?

Majalisar Tarayyar Najeriya ta soke shirinta na komawa bakin aiki, lamarin da zai haifar da tsaiko kan duba bukatun da bangaren shugaban kasa ya gabatar mata na kasafin kudin hukumar zabe da kuma gibin kasafin kudin kasa, yayin da wasu ke ganin cewa, soke zaman na da nasaba da fargabar makarkashiyar tsige Sanata Bukola Saraki daga kujerar shugaban Majalisar Dattawa bayan komawarsa jam’iyyar PDP mai adawa daga APC mai mulki.

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki tare da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara.
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki tare da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara. NigerianEye
Talla

'Yan majalisun sun ce, ba za su yi gaggawar amincewa da bukatar shugaba Muhammadu Buhari kan kudin zaben ba duk da cewa tun a ranar 17 ga watan Yuli ya gabatar da bukatar.

Rahotanni na cewa, watakila a samu tsaikon amincewa da bukatar har nan da ranar 25 ga watan Satumba mai zuwa, wato lokacin da ake saran komawar ‘yan majalisun bakin aiki.

A makon jiya ne, shugaban Hukumar Zaben Kasar mai zaman kanta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya gana da majalisar wadda ya shaida mata cewa, hukumar ta ajiye ranar 15 ga watan Agusta a matsayin ranar fara gudanar da ayyukanta na zaben 2019, kuma hukumar na bukatar kudi don gudanar da ayyukan.

Shugaba Buhari ya bukaci majalisar da ta amince da Naira biliyan 242.445 don ayyukan INEC da sauran hukumomin tsaro don zaben 2019, amma daga cikin kudaden za a ware Naira biliyan 164.1 don cike gibin kasafin 2018.

A makon jiya ne mataimakin kakakin majalisar wakilai, Yusuf Suleimon Lasun ya sanar cewa, majalisar za ta koma bakin aiki a cikin wannan makon don amincewa da kasafin kudin zaben na 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.