Isa ga babban shafi
Najeriya

Za'a daure karin wadanda suka sace dukiyar 'yan Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sha alwashin kamawa tare da hukunta karin manyan jami’ai da ‘yan siyasar da suka jefa tattalin arzikin kasar cikin mummunan hali ta hanyar wawashe kudaden al’umma.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Daniel Leal-Olivas/ Reuters/File Photo
Talla

Shugaba Buhari wanda ya koma gida da yammacin jiya Asabar, bayan ya kare hutun da ya dauka a London ya sha alwashin ne yayin ganawa da manema labarai a filin jragen sama na Abuja, kafin isa fadar gwamnati.

Shugaban ya ce ‘yan Najeriya suna yi masa kyakkyawan zaton zai tabbatar da an hukunta wadanda suka yi sama da fadi da kudadensu, kuma tabbas ba zai watsa musu kasa a ido ba, domin ba shakka hukunta wadanda suka yi wadaka da kudaden al'umma ya zama tilas.

A ranar 3 ga watan Agusta, 2018, shugaba Buhari ya fara hutun kwanaki 10 a birnin London, inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar a matsayi mukaddashin shugaba.

Daga cikin muhimman ayyukan da mataimakin shugaban Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo ya zartar akwai sauya shugabancin hukumar jami’an tsaron farin kaya ta DSS, inda ya maye gurbin Lawal Daura da Mista Matthew Seiyefa.

Korar Lawal Daura daga mukaminsa ya biyo bayan umarnin da ya baiwa jami’an hukumar ta DSS na datse kofar shiga majalisun Najeriya a farkon watan Agusta , lamarin da haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar.

Farfesa Osinbajo, ya kuma bada umarnin sauya fasalin shugabanci da ayyukan rundunar ‘yan sandan kasar ta musamman mai yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka wato SARS.

Bayarda umarnin yi wa rundunar ta SARS garambawul ya biyo bayan koken jama’a da ya yawaita, kan yadda jami’an ‘yan sandan da ke karkashin rundunar ta SARS ke cin zarafin mutane yayin gudanar da ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.