Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kashe shugabansu

Majiyoyi kwarara sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, mayakan Boko Haram sun kashe shugabansu da ke jagorancin wani bangare na kungiyar, Mamman Nur.

Abu Musab Al-Barnawy da ke jagorancin bangaren Mamman Nur
Abu Musab Al-Barnawy da ke jagorancin bangaren Mamman Nur Guardian Nigeria
Talla

Majiyoyin da ke da cikakkiyar masaniya game da Boko Haram sun ce, wasu jiga-jigan makusantansa ne suka kashe shi a ranar 21 ga watan Agusta biyo bayan rashin gamsuwa da salon jagorancinsa, musammam ganin yadda yake da rauni idan aka kwatanta shi da Abubakar Shekau.

A shekarar 2014 ne, Mamman Nur ya jagoranci boren da mayakan suka yi wa shugabansu Abubakar Shekau har aka samu tsagin shugabancin Abu Mus’ab Al-Barnawy.

Koda dai wasu majiyoyin na cewa, Mamman Nur ne hakikanin shugaban tsagin na Al-Barnawy, kawai dai ya mika masa ragama ne saboda darajar mahaifinsa, Mohammed Yusuf da aka kashe a shekarar 2009.

sunan Al-Barnawy dai “Habib”, kuma mahaifinsa ne ya assasa kungiyar ta Boko Haram.

Kwo yanzu, rundunar sojin Najeriya ba ta tabbatar da mutuwar Nur ba wanda aka kashe matarsa a wani samame da rundunar ta kai maboyar kungiyar a yankin tafkin Chadi a cikin watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.