Isa ga babban shafi
Najeriya

Cutar kwalara ta hallaka mutane 97 a Najeriya - MDD

Wani rahoton majalisar dinkin duniya ya ce barkewar cutar kwalara, ko amai da gudawa a arewa maso gabashin Najeriya, yayi sanadin rasa rayukan akalla mutane 97, cikin makwanni biyu da suka gabata zuwa yanzu.

Cutar kwalara ta yi sanadin mututwar sama da mutane 500 a Yankin Tafkin Chadi.
Cutar kwalara ta yi sanadin mututwar sama da mutane 500 a Yankin Tafkin Chadi. AFP Photo/NATASHA BURLEY
Talla

Majalisar ta ce a halin da ake ciki, an samu rahotannin kamuwar sama da mutane 3000 da cutar ta kwalara a jihohin Borno da Yobe.

Ofishin bada agajin jin kai na majalisar OCHA ya ce zuwa yanzu yawan wadanda suka kamu da kwalarar, ya kai dubu 3, 126, tun bayan shelar barkewar cutar a jihar Borno makwanni biyu da suka gabata.

A ranar larabar da ta gabata, Majalisar dinkin duniya ta fitar da rahoton cewa, sama da mutane 500 sun hallaka a dalilin kamuwa da cutar kwalara a yankin Tafkin Chadi daga farkon shekarar da muke ciki zuwa yanzu.

Ofishin na OCHA ya kara da cewa, akwai fargabar mutane miliyan shidda za su iya kamuwa da cutar ta kwalara a yankin na Tafkin Chadi, muddin ba’a dauki matakan gaggawa ba na dakile cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.