Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Legas ta kwace shanu da ragunan makiyaya

Gwamnatin Jihar Legas da ke Kudancin Najeriya ta kwace shanu akalla 30 da raguna 10 bayan ta same su suna zirga-zirgar kiwo ba bisa ka’ida ba a kan babbar hanyar unguwar Lekki.

Gwamnatin Jihar Legas ta haramta kiwon dabbobi a kan hanyoyi
Gwamnatin Jihar Legas ta haramta kiwon dabbobi a kan hanyoyi starconnectmedia.com
Talla

Gwamnatin Jihar ta ce, ba za ta amince da irin wannan kiwon ba, kuma ta gargadi makiyaya da su kauce wa kiwon dabbobinsu akan hanyoyi saboda a cewarta, hakan na barazana ga al’ummar jihar musamman masu kai-kawo akan hanyoyin.

Sakataren din-din-din a Ma’aikatar Gona ta Jihar, Olayiwola Onasanya ya shaida wa manema labarai cewa, a shirye suke su mika dabbobin da suka kwace muddin mamallakansu sun amince su biya tarar kudade ga gwamnati.

Onasanya ya ce, za su tabbatar da rashin sake aukuwar irin wannan zirga-zirgar dabbobin ba bisa ka’ida ba a jihar, in da ya ce jami’an gwamnati na musamman za su ci ga ada sanya ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.