Isa ga babban shafi
Najeriya

Ko mutuwar Badeh ta kawo karshen tuhumarsa?

‘Yan Najeriya da suka hada da jiga-jigan ‘yan siyasa na ci gaba da bayyana alhininsu da mutuwar tsohon Babban Hafson Tsaron Kasar, Alex Badeh da wasu ‘yan bindiga suka kashe shi a kan hanyar Abuja da Keffi bayan ya fito daga gonarsa.

Marigayi Alex Badeh
Marigayi Alex Badeh Daily Trust
Talla

Kisan Badeh na zuwa ne a dai dai lokacin da yake fuskantar tuhuma kan zargin karkatar da kudaden sayen makamai.

Koda yake ya musanta wannan zargin da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasar, EFCC ke yi masa, yayin da aka shirya sake bayyanarsa a gaban kotu a ranar 16 ga watan Janairu mai zuwa don kare kansa kan sauran tuhumar da ake yi masa.

Darektan Sahen Hulda da Jama’a da kuma Yada Labarai na Rundunsar Sojin Sman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya tabbatar da mutuwar Badeh da direbansa a cikin wata sanarwa sakamakon raunin bindiga.

Marigayi Badeh ya mutu yana da shekaru 61 kuma ya fara aikin soji ne a hukumance tun shekarra 1979.

An haife shi a garin Vintim da ke karamar hukumar Mubi a jihar Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, yankin da ke fama da rikicin Boko Haram.

A cikin watan Oktoban shekarar 2012 ne, tsohn shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya nada Badeh a matsayin hafsan sojin saman Najeriya kafin daga bisani a ba shi mukamin hafson tsaron kasar a cikin watan Afrilun shekarar 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.