Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu tunatar da 'yan Najeriya alkawuranmu na 2015 - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari, ya ce har yanzu yana nan akan bakansa na neman ‘yan kasar su bashi damar inganta fannoni uku da ya maida hankali kansu a lokacin yakin neman zabensa na shekarar 2015.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Reuters
Talla

A cewar shugaba Buhari yakin neman 'yan Najeriya su sake bashi dama a shekarar 2019, zai mayar da hankali kan fannonin inganta tsaro, tattalin arziki da kuma yakar cin hanci da rashawa, wadanda ya ce har yanzu, batutuwa ne da ke bukatar jajircewa wajen magance matsalolinsu.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake sanar da cewa nan bada jimawa ba, zai kaddamar da yakin neman zabensa na shekarar 2019 gadan gadan, domin jagorantar kasar wa’adi na biyu, a lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin addini, masu rike da sarautun gargajiya da sauran ma’aikatan gwamnati, a fadar gwamnati da ke garin Abuja.

Shugaban Najeriyar, ya ce yayin yakin neman zabensa da zai kaddamar nan bada jimawa ba, zai mayar da hankali wajen tunatar da ‘yan Najeriya alkawuran da ya dauka a shekarar 2015.

Dangane da sukar cewa shugabancinsa na jan kafa wajen daukar matakan da suka dace akan lokaci kan wasu batutuwa kuwa, inda wasu ke kiransa da ‘Baba Go Slow’ a turance, shugaba Buhari ya ce an sanya masa sunan ne, saboda jajircewarsa wajen tabbatar da an kwato kudaden ‘yan Najeriya da aka sace, matakin da ya ce ba zai janye daga kai ba, komai tsawon lokacin da zai dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.