Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari ya rasu

Rahotanni daga Najeriya na cewa Allah ya yi wa tsohon shugaban kasar a Jamhuriya ta biyu, Alhaji Shehu Usman Shagari rasuwa a yammacin ranar Juma'a a birnin Abuja.

Shehu Shagari ya rasu yana da shekaru 93.
Shehu Shagari ya rasu yana da shekaru 93. dailypost
Talla

Marigayi Alhaji Shehu Shagari wanda shi ne Turakin Sokoto ya yi mulkin Najeriya tsakanin shekara ta 1979 zuwa 1983.

Ya mutu yana da shekaru 93 bayan rashin lafiya a babban Asibitin Abuja.

Ya yi Malamin makaranta kafin ya shiga harkokin siyasa a shekara ta 1951 kafin a zabe shi a matsayin dan Majalisar Wakilai a shekara ta 1954.

Marigayin ya kasance shugaban Najeriya na 6 kuma Olusegun Obasanjo ne ya mika masa mulki a shekara ta 1979.

Shugaban Najeriya mai ci yanzu, Muhammadu Buhari ne ya karbe iko daga gwamnatin Shagari sakamakon matsalolin da suka shafi yawaitan cin hanci da rashawa, kamar yadda majalisar zartaswar sojin kasar ta waccan lokaci ta amince tare da bada dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.