Isa ga babban shafi
Najeriya

Muhimman abubuwan da ke gaban Najeriya a 2019

A yayin da aka shiga sabuwar shekara ta 2019, Najeriya kamar sauran kasashen duniya na da muhimman abubuwan da ke gabanta. Za mu duba wasu daga cikinsu.

Fafatawar da za a yi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar na cikin manyan abubuwan da za su wakana a sabuwar shekara a Najeriya
Fafatawar da za a yi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar na cikin manyan abubuwan da za su wakana a sabuwar shekara a Najeriya Photo: Pius Utomi Ekpei/AFP
Talla

ZABEN 2019

Babu shakka zaben gama-gari na daya daga cikin muhimman abubuwan da za su wakana a shekarar 2019 a Najeriya, in da al’ummar kasar za su halarci rumfunan zabe a cikin watan Fabairu don kada kur’iunsu ga ‘yan takarar manyan jam’iyyun siyasar kasar biyu, wato shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da abokin fafatawarsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Koda yake akwai sauran ‘yan takara daga sauran jam’iyyun adawa da za su fafata da Buhari, amma hankuka za su fi karkata ne kan APC da PDP saboda dimbin magoya bayan da kowanne bangare ke tinkaho da su a sassan kasar.

Kazalika a cikin watan na Fabairu ne za a gudanar da zaben ‘Yan Majalisar Tarayyar kasar kamar yadda Hukumar Zaben Kasar, INEC ta tsara.

Bayan zaben na shugaban kasa da na ‘Yan Majalisar Tarayya, al’ummar Najeriya za su sake yin dandazo a rumfunan zabe a cikin watan Maris don kada kuri’u ga ‘yan takarar kujerun gwamnoni da na ‘Yan Majalisar Jihohi.

Tuni aka fara tarukan gangamin yakin neman zabe a kasar, yayin da ake ci gaba da tafka muhawara ta kafafen yada labarai tsakanin ‘yan takara daban-daban.

RIKICIN BOKO HARAM

Hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaddamarwa a sassan Najeriya da sauran kasashe makwabta na ci gaba da daukan hankula. Koda yake gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na ikirarin samun nasara akan ‘yan ta’addan, yayin da rahotanni daban daban suka tabbatar da munanan kwantar-baunar da mayakan suka kaddamar kan jami’an tsaro musamman a yankin arewa maso gabashin kasar, in da rikicin ya fi kamari.

Babu shakka al’ummar Najeriya musamman mazauna yankin arewa maso gabashin kasar, na fatan ganin an kakkabe mayakan Boko Haram baki daya a cikin wannan shekara ta 2019 don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa wanda zai kai ga habbaka harkokin kasuwanci da tattalin arzikin jama’a.

A baya-bayan nan, rundunar sojin kasar ta sanar da shirinta na fara wani gagarumin aikin lugudan wuta kan maboyar mayakan na Boko Haram a garin Baga da ke jihar Borno , in da tuni aka fara kwashe mazauna garin da ‘yan gudun hijira.

MAFI KARANCIN ALBASHIN MA'AIKATA

Akwai yiwuwar Kungiyar Kwadagon Najeriya ta sake tsunduma cikin wani gagarumin yajin aikin gama-gari a cikin sabuwar shekarar 2019 don tilasta wa gwamnatin kasar amincewa da bukatarta ta biyan dubu 30 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata a kasar.

Kungiyar ta NLC ta sanar da gwamnatin kasar cewa, za ta kira sabon yajin aiki nan da ranan 8 ga watan Janairun sabuwar shekara muddin ba a biya mata bukatarta ba.

Da dama daga cikin gwamnoni jihohin kasar sun bayyana cewa, ba su da karfin biyan Naira dubu 30 a matsyin mafi karancin albashin ma’aikata, abin da ka iya tsananta rashin jituwa tsakanin NLC da gwamnatin Najeriya a wannan shekara.

SHARI'AR MASU CIN HANCI DA RASHAWA

Akwai shari’o’i da dama kan wadanda ake zargi da cin hanci da rashawa da ake saran kammala su a cikin sabuwar shekarar 2019 a Najeriya.

Ana saran kammala shari’ar da aka kwashe tsawon shekaru 11 ana yi wa tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashid Ladoja da ake zargi da almundahanar kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 4.7.

Mai shari’a Mohammed Idris, ya tsayar da ranar 18 ga wannan wata na Janairu a matsayin ranar sake zaman sauraren shari’arsa kafin daga bisani a sanar da ranar yanke hukunci.

Shi ma tsohon gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu zai san makomarsa kan tuhumar da ake yi masa ta karkatar da Naira biliyan 7.65. An shafe shekaru 12 ana gudanar da wannan shari’a, yayin da ake dakon tsohon gwamnan ya kare kansa a gaban kotu a cikin wannan shekara.

A cikin watan Oktoban bara ne Kotun Tarayyar Najeriya ta tsare tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose kan zargin sa da ruf da ciki da Naira biliyan 2.2 karkashin mai shari’a Mojisola Olatoregun a birnin Legas.

Sai dai mai shari’ar za ta yi ritaya a cikin wannan shekara bayan ta cika shekaru 65.

Ko shin za a kammala shari’ar Fayose kafin ritayarta a wannan shekara?

YAJIN AIKIN ASUU

Har yanzu babu tsayayyiyar ranar da daliban jami’o’in Najeriya za su koma azuzuwa sakamakon yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’in ta tsundima bayan gwamnati ta ki cika alkawuran da ta yi mata.

Tun a ranar 5 ga watan Nuwamban bara ne, ASUU ta tsundima cikin yajin aikin, amma watakila ta janye a cikin wannan shekarar bayan cimma matsaya da gwamnati .

Wadannan kadan ne daga cikin muhimman abubuwan da ke gaban Najeriya a cikin wannan sabuwar shekara ta 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.