Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu hallaka masu katsalandan a zaben Najeriya- El-Rufa'i

Gwamnan Jihar Kaduna da ke Najeriya, Nassir El-Rufai ya yi barazanar cewa, jami’an tsaron kasar za su hallaka sojojin kasashen ketare da suka yi katsalandan cikin al’amuran zaben kasar.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i The Nation
Talla

Kalaman El-Rufa’i na zuwa ne bayan sama da mako guda da gwamnatin Najeriya ta zargi manyan kasashsen duniya da suka hada da Amurka da Birtaniya da Kasashen Turai da yunkurin katsalandan a zaben.

Kasashen sun soki matakin shugaba Muhammdu Buhari na dakatar da Walter Onnoghen daga kujerar alkalin alkalan Najeriya, in da suka gargadi cewa, matakin zai yi tasiri kan sahihancin zaben shugabancin kasar mai zuwa.

A yayin zantawa da kafar talabijin din kasar, NTA, El-Rufai ya ce, “Wadanda ke kiran wasu da su zo su tsoma baki a Najeriya, muna jiran zuwansu, za su koma gida a cikin makara”

Gwamnan ya ce, Najeriya ba za ta sallama ‘yancinta ga wasu manyan kasashen duniya ba.

Masana siyasa na hasashen cewa, zaben na watan Fabairu zai yi zafi sosai, yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke zargin jam’yyar APC mai mulki da kitsa magudi a lokacin zaben.

Koda yake shugaba Buhari ya sha nanata kudirinsa na gudanar da sahihin zabe a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.