Isa ga babban shafi
Najeriya

Tilas INEC ta sauya matsayin kan makomar APC a Zamfara - Yari

Yayinda rage kwanaki kalilan a gudanar da zabukan Najeriya, gwamnan Zamfara, Abdul Aziz Yari yayi barazanar cewa, babu wani zabe da zai gudana a matakin jihar, muddin hukumar INEC ba ta baiwa jam’iyyar APC mai mulki damar tsayar da ’yan takararta ba.

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari.
Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari. RFIHAUSA
Talla

Yari yayi ikirarin ne a karshen mako, yayin yakin neman zaben da ya halarta a karamar hukumar Talata Mafara.

A makon daya gabata hukumar zaben Najeriya ta jaddada matsayinta kan haramtawa APC tsaida ‘yan takara a zabukan Jihar Zamfara, saboda saba ka’idar gudanar da zabukan fidda gwani da tayi, na rashin kamala su kafincikar wa’adin da hukumar zaben ta debawa jam’iyyu.

A ranar Juma’a 25 ga watan Janairu, babbar kotun Zamfara da ke Gusau, ta yanke hukuncin tabbatar da zaben fidda gwanin Jam’iyyar APC a jihar, wanda ya gudana a ranakun 3 da 7 ga watan Oktoban shekarar 2018.

Kotun ta kuma umarci hukumar zaben Najeriya INEC, ta amince da zaben fidda gwanin na APC da ya shafi mukamin gwamna, ‘yan majalisun dokokin tarayya da kuma na dokokin jihar.

Sai dai a rana guda kuma, babbar Kotun Najeriya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa hukumar INEC tana da ikon kin karbar 'yan takarar jam'iyyar APC a zabukan na jihar Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.