Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba ma goyon bayan dage zabukan Najeriya - APC

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, ta bayyana bacin ranta kan matakin dage zabukan kasar da hukumar INEC ta sanar.

Daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Festus Keyamo.
Daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Festus Keyamo. The Herald Nigeria
Talla

APC ta hannun daraktan yada labaran kwamitin yakin neman zabenta Festus Keyamo ta yi amfani da kakkausan harshe wajen sukar sauya ranakun zaben, inda ta bukaci magoya bayanta su yi hakuri tare da jajircewa wajen ci gaba da mara musu baya.

A cewar Keyamo tilas jam’iyyar APC ta bayyana rashin jin dadinta la’akari da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari, ta baiwa hukumar zaben Najeriyar INEC, dukkanin hadin kai da ta bukata, na samar da kudade da kayan aiki, domin tabbatar da sahihin zabe akan lokaci, amma duk da haka aka fuskanci wannan tsaiko.

Kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar ta APC ya kara da cewa, yana fatan hukumar INEC za ta ci gaba da zama mai adalci ga dukkanin jam’iyyun Najeriya, domin karyata jita-jitar da wasu ke yadawa cewa ta dage zaben ne domin taimakawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP, wadda bata shiryawa zabukan kasar da aka tsara somawa daga ranar 16 ga watan Fabarairu ba.

A halin yanzu zaben shugaban kasa dana 'yan majalisun wakilai da dattijai zai gudana a ranar 23 ga watan Fabarairu, yayinda na gwamnoni da na 'yan majalisun dokokin jiha zai gudana ranar 9 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.