Isa ga babban shafi
Najeriya

Duk wanda ya saci akwatin zabe zai iya rasa ransa - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya baiwa jami’an tsaron kasar, da suka hada da sojoji da ‘yan sanda, umarnin daukar mataki mai karfi, wajen murkushe duk wanda yayi yunkurin aikata magudi a zabukan kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gargadi masu yunkurin aikata magudi a zabukan kasar na 2019 ne, yayin taron da ya jagoranta na 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya gargadi masu yunkurin aikata magudi a zabukan kasar na 2019 ne, yayin taron da ya jagoranta na 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC. REUTERS/ Afolabi Sotunde
Talla

Buhari ya bada umarnin ne yayinda hukumar zaben kasar INEC da sauran masu ruwa da tsaki, ke shirin zabukan kasar da aka sauya ranakun gudanar da su daga 16 ga Fabarairu da 2 ga watan Maris, zuwa 23 ga watan Fabarairu da kuma 9 ga watan Maris.

Yayinda ya ke ganawa da shugabanni da wakilan jam’iyyarsa mai mulki ta APC a Abuja, shugaba Buhari ya yi gargadin cewa, duk wanda yayi gangancin haddasa rikici, aikata abinda zai wargaza shirin gudanar da sahihin zaben 2019, ko satar akwatin zabe, zai iya zama laifi na karshe da zai aikata don cutar da al’umma, domin zai jefa rayuwarsa cikin hadari, kasancewar jami’an tsaro suna da izinin daukar matakin da ya dace mai tsauri na hukuntashi.

Shugaban Najeriyar ya ce ya baiwa jami’an tsaron kasar da su tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun kada kuri’unsu ba tare da fuskantar tsangwama ba, ta kowace fuska.

Kafin wannan lokacin dai, an dade ana musayar yawu tsakanin jam’iyyar APC mai mulki, da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, bisa zargin junansu da yunkurin yin magudi a zabukan 2019, ta hanyar sayen kuri’a ko katunan zabukan ‘yan Najeriya.

Ranar Asabar, 16 ga watan Fabarairu hukumar INEC ta dage zaben shugaban kasa, da kuma na ‘yan majalisun wakilai da dattijai, yayinda ya rage awanni kalilan a soma kada kuri’a.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce, babu siyasa a batun dage zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisun.

Farfesan ya ce, sun dauki matakin dage zabukan a hukumance bayan ganawa da masu ruwa da tsaki, inda ya ce matsalar isar da kayayyaki zabe da kuma gobarar da ta tashi a wasu ofisoshin INEC na cikin dalilan dage zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.