Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

MDD ta yi alhinin cika shekara 1 da kisan jami'anta a Rann

Ofishin lura da ayyukan bada agajin jinkai na majalisar dinkin duniya, yayi taron alhinin cika shekara guda da mutuwar ma’aikatansa, da mayakan Boko Haram suka hallaka a garin Rann da ke jihar Borno, ranar 1 ga wata Maris na 2018.

Motocin asibiti da suka dauko gawarwakin ma'aikatan bada agajin jin kai na Majalisar dinkin duniya da mayakan Boko Haram suka hallaka a garin Rann. 2/3/2018.
Motocin asibiti da suka dauko gawarwakin ma'aikatan bada agajin jin kai na Majalisar dinkin duniya da mayakan Boko Haram suka hallaka a garin Rann. 2/3/2018. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Shugaban ofishin bada agajin jin kan na Majalisar dinkin duniya da ke Najeriya, Mr Edward Kallon, ya yi alla wadai da kisan ma’aikatan tare da bukatar sakin ma’akaciyarsu guda Alice Loksha da har yanzu mayakan na Boko Haram ke rike da ita.

Yayin harin na shekarar bara kan garin na Rann, bayaga hallaka ma’aikatan agajin, mayakan Boko haram sun sace wasu 3, a watan Satumba da kuma Oktoban shekarar ta 2018 kuma suka hallaka biyu daga ciki, Saifura Khorsa da kuma Hauwa Liman.

Mista Kallon, ya ce harin na Rann, ya girgiza ilahirin kungiyoyin bada agajin gaggawa da ke aiki a sassan duniya, musamman ganin yadda lamarin ya shafi masu kananan shekaru da ke kokarin tasawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.