Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya na dakon sakamakon zaben gwamnoni

A Najeriya, an soma kidayar kuri’un da aka kada a zaben Gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, inda zaben kujerun Gwamnonin ya gudana a jihohi 29, na ‘yan majalisun kuma a ilahirin jihohin kasar 36.

Jami'in hukumar zaben Najeriya, yayin kidayar kuri'un zaben Gwamna da 'Yan Majalisun jiha a daya daga cikin rumfunan zabe a jihar Legas. 9/3/2019.
Jami'in hukumar zaben Najeriya, yayin kidayar kuri'un zaben Gwamna da 'Yan Majalisun jiha a daya daga cikin rumfunan zabe a jihar Legas. 9/3/2019. REUTERS/Adelaja Temilade
Talla

A mafi akasarin sassan Najeriyar dai, zabukan sun gudana cikin kwanciyar hankali, sai dai a wasu bangarorin, an fuskanci matsalolin yiwa masu kada kuri’a da jami’an zabe barazana, sayen kuri’u da kuma, rasa rayuka.

Gamayyar kungiyoyi na ciki da wajen Najeriya da ke sa ido kan zabukan kasar sun bayyana rahotannin mutuwar mutane 7 kan zabukan na ranar Asabar

Sauran jihohin da aka fi fuskantar matsalolin rikici, tare da hasarar rayuka sun hada da Bayelsa da Ebonyi da kuma Legas.

A Bayelsa da Ebonyi, rahotanni sun ce an samu hasarar rayukan mutane 2 a kowace jiha, yayinda a Legas aka kone ababen ahawa akalla 35 tare da hallaka wasu mutane 2 a wasu sassan jihar, kamar yadda jami’an sa ido kan zabukan Najeriyar suka tabbatar.

A Rivers kuwa, tsohon gwamnan jihar kuma ministan sufuri a yanzu, Rotimi Amechi ya ce mutane 3 sun rasa rayukansu a rikicin zabe.

A bangare guda kuma, kakakin hukumar zaben Najeriya na jihar Rivers, ya shaidawa kamfanin daillancin labarai na AFP cewa wasu tsageru sun yi garkuwa da jami’ansu, sai dai bai bayyana adadinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.