Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Jami'an tsaro sun kame 'yan daba a Kano

Mataimakin Sifeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, DIG Anthony Ogbizi Micheal, ya bayyana kame wasu mutane 10 a Kano, da ake zargin suna cikin gugun ‘yan dabar da suka tayar da hankulan jama’a a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa, yayin kada kuri’a a karashen zaben Gwamna da aka yi a yau Asabar.

Wasu jami'an Yan Sandan Najeriya.
Wasu jami'an Yan Sandan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Yayin bayyana kamen, DIG Micheal ya musanta rahotannin da ke cewa akwai wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hargitsin da ‘yan dabar suka haddasa a mazabar ta Gama, inda ya zargi marasa kishin kasa da yada labaran karya ta hanyar amfani da kafofin sadarwa na zamani.

Rahotanni daga jihar Kanon dai sun tabbatar da cewa gungun ‘yan bangar siyasa dauke da makamai sun bayyana a mazabar Gama da ke karamar hukumar Nasarawa, inda suka rika kai komo kan babbar hanyar yankin.

‘Yan bangar sun hana jami’an sa ‘ido da manema labarai gudanar da aikinsu a yankin, daga bisani kuma hargistin da ya tashi ya tilastawa mutane da dama tserewa, ciki har da wakilinmu da ya tsallake rijiya da baya.

Sauran jihohin da Jihohin INEC ta gudanar da karashen zaben sun hada da Sokoto, Filato, Benue da kuma Bauchi bayan da Hukumar ta bayyana zaben jihohin a matsayin wadanda ba su kammala a ranar 9 ga wannan wata na Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.