Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Najeriya sun kai farmaki kan sansanin yan bindiga

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da lalata sansanin daya daga cikin manyan shugabannin yan bindigar da suka addabi jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin kasar, Alhaji Lawal.

Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. AFP / STEFAN HEUNIS
Talla

Farmakin jiragen yakin, yayi nasarar hallaka 20 daga cikin mayakan na Alhaji Lawal da ke sansanin a gaf da dajin Rugu da ke jihar Zamfara.

Kakakin rundunar sojin saman ta Najeriya Ibikunle Daramola ne ya bayyana samun nasarar Yau Talata a birnin Abuja.

Rundunar sojin ta Najeriya ta ce sansanin, matattara ce da yan bindigar ke ajiye ababen hawa, makamai da kuma kayan abinci, zalika suna amfani da sansanin wajen kaddamar da hare-hare kan sassan jihar Zamfara.

Farmakin jiragen yakin na Najeriya ya zo ne bayan da a ranar Asabar da ta gabata, rahotanni suka ce gungun yan bindiga sun hallaka akalla mutane 30 a wani farmaki da suka kai kan kauyen Dungurgu.

Sai dai kakakin rundunar yan sandan Zamfara SP Muhammad Shehu ya ce mutane 10 ne suka hallaka a farmakin yan bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.