Isa ga babban shafi
Najeriya

Dattawan arewacin Najeriya sun soki Buhari kan tsaro

Shugaban Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi ya bayyana cewa, matsalar tsaro a arewacin Najeriya ta fi muni a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari fiye da zamanin mulkin Goodluck Jonathan.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Farfesa Ango wanda tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ne da ke Zaria, ya ce, shugaba Buhari ba ya tabuka abin kirki wajen magance matsalar kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

Farfesa Ango dai na mayar da martani ne game da tsokacin da mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu ya yi a yayin zantawa da gidan talabijin na AIT a shirin Kakaaki, in da ya ce, kasancewar shugaban kasar ya fito daga garin Daura, hakan ba ya nufin ba za a iya aikata mummunan laifi a Daura ba ko kuma a ba ta fifiko na musamman”

Shehu na magana ne dangane da sace Surukin Buhari, Alhaji Musa Uba da ‘yan bindiga suka yi awon gaba da shi a Daura.

Shehu ya ce, gwamnatin shugaba Buhari na aiki tukuru wajen magance ta’adanci a kasar.

Ko a cikin watan jiya, sai da Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ce, za a ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga a Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto muddin ba a tanadi yanayin aiki mai kyau ga jami’an ‘yan sanda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.