Isa ga babban shafi
Najeriya

Dubban 'yan tawayen Niger Delta sun amfana da shirin "Amnesty"

Mashawarci na musamman ga shugaban Najeriya kan shirin afuwa a yankin Niger Delta, Farfesa Charles Dokubo ya bayyana cewa, adadin tsoffin ‘yan tawayen yankin da suka kammala karatun jami’a, ya aki dubu 20,kuma har yanzu akwai dubban tsoffin ‘yan tawayen da ke ci gaba da cin gajiyar shirin a fannoni da dama.

'Yan tawayen Niger Delta
'Yan tawayen Niger Delta AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Farfesa Dokubo ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu akwai tsoffin ‘yan tawayen na Niger Delta dubu 2 da 577 da ke ci gaba da karatu da suka hada da dubu 1 da 60 da ke jami’o’i akalla 10 a cikin Najeriya, yayinda kuma dubu 1, 517 ke karatu a sama da jami’oi’ 50 a sassan Turai da Asiya da Afrika har ma da Amurka.

Dokubo ya kara da cewa, ya zuwa bara, Shirin Afuwar da aka fi sani da “Amnesty Programme a Turance” ya taimakwa tsoffin ‘yan tawayen dubu 4 da 450 wajen kafa kanana da matsakaitan sana’o’i.

Ana dai kashe akalla Naira biliyan 65 zuwa biliyan 67 a kowacce shekara a karkashin wannan shiri kamar yadda Dokubo ya bayyana a birnin Abuja, yayinda ya jaddada cewa, har yanzu akalla tsoffin ‘yan tawaye dubu 30 na kan cin gaciyar shirin. Sannan kuma gwamnatin tarayya na ci gaba da biyan albashin dubu 65 ga tsoffin ‘yan tawayen.

Nan gaba dai, Shirin Afuwar zai mayar da hankali ne kan samar da guraben aiki ga tsoffin ‘yan tawayen da suka kammala karatu domin ci gaba samun albashi mafi tsoka a cewar Dokubo.

Mashawarcin na shugaban kasa, ya karkasa fannonin da tsoffin ‘yan tawayen suka kware akai da suka hada da noma da kanikanci da walda da aikin kafinta da da aikin wutar lantarki.

Sauran bangarorin sun hada da fasahar sadarwar zamani da kiwon lafiya da tsaftar muhalli, yayinda wasunsu suka kware a harkar zirga-zirgar jiragen sama da kuma kera jiragen ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.