Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Buhari za ta fitar da 'yan Najeriya miliyan 100 daga talauci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta fitar da ‘yan kasar miliyan 100 daga cikin kangin talauci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari jim kadan da shan rantsuwar kama aiki a sabon wa'adinsa na biyu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari jim kadan da shan rantsuwar kama aiki a sabon wa'adinsa na biyu Ng.gov.jpg
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar jawabin kaddamar da bikin ranar dimokaradiyyar Najeriya ta 12 ga watan Yuni a birnin Abuja.

Buhari ya ce, gwamnatin APC za ta jajirce wajen cimma burin magance wa ‘yan kasar akalla miliyan 100 talauci cikin shekaru 10 masu zuwa.

Shugaban Najeriyar ya kara da cewa yanzu haka, adadin kudaden kasar da ke asusun ajiyarta na kasashen ketare ya karu zuwa Dala biliyan 45.

Alkawarin gwamnatin APC na zuwa ne, kwanaki kadan bayan da wani rahoton hadin gwiwar Bankin Duniya da Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF da kuma Majalisar Dinkin Duniya, ya ce mutane miliyan 91 ke fama da matsanancin talauci a Najeriya.

Kididdigar ta kara da hasashen cewa, a kowane minti daya, akwai ‘yan Najeriya akalla 6 da suke afkawa cikin bala’in talauci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.