Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kai sabon farmaki kan sojan Najeriya

Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun halaka sojojin kasar da dama tare da kwashe tarin makamai, bayan wani samame da suka kai makwancin sojan dake kan iyakan kasar da Nijar.

Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya.
Wasu dakarun rundunar sojin Najeriya. AFP/Audu Marte
Talla

Wasu kafofin yada labarai sun rawaito cewa mayakan kungiyar ta Boko Haram na tsagin da yayiwa IS dake Yammacin Afrika mubaya’a, cikin motocin a kori kura 8 ne suka kaiwa sansanin sojan farmaki, da ke kauyen Kareto mai tazarar kilomita 335 da arewacin birnin Maiduguri.

Majiyoyin sun ce mayakan na Boko Haram sun ci karfin sojan na Bataliya ta 153 bayan gwabza fada sosai.

Wani soja da ya nemi a sakaya sunansa ya gaskata harin a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

A nata bangaren, majiyar sojan Najeriya ta ce dakarun kasar da aka rasa, har da wani mai mukamin Laftanar Kanal da ke jagorantar sojan da suka fafata da mayakan.

Harin na baya bayan nan ya zo ne Makwanni biyu bayanda mayakan na Boko Haram suka kai kazamin hari kan wani sansanin sojan Najeriya dake jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.