Isa ga babban shafi
Najeriya

'Matsayin Shari’a kan hukuncin haramta kungiyar Shi’a'

Wata Kotu a Najeriya ta amince da bukatar gwamnatin kasar na haramta ayyukan kungiyar Yan uwa Musulmi ta mabiya Shi’a saboda abinda ta kira alaka da ayyukan ta’addanci.

Jami'in tsaron Najeriya rike da wani matashi dan kungiyar Yan Uwa Musulmi IMN a Abuja, bayan zanga-zangar neman tilasta sakin jagoransu Shiekh Ibrahim Zakzaky.
Jami'in tsaron Najeriya rike da wani matashi dan kungiyar Yan Uwa Musulmi IMN a Abuja, bayan zanga-zangar neman tilasta sakin jagoransu Shiekh Ibrahim Zakzaky. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Matakin na zuwa ne kwanaki bayan arangamar da aka yi wadda ta kai ga rasa rayukan mutane da dama a Abuja, cikinsu harda mataimakin kwamishinan Yan Sanda.

Sai dai hukuncin kotun na haramta kungiyar ta mabiya Shi’a ya haifar da muhawara mai zafi dangane da dacewa ko akasin yanke hukuncin, muhawarar ta kuma fadada zuwa kan batun cewa ko kotu na da hurumin yanke irin wannan hukunci.

Dangane da hukuncin kotun, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin shari’a, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami’ar Abuja.

Yayin tattaunawar, Farfesa Shehu Abdullahi Zuru wanda ya ce kotu na da hurumin yanke hukuncin da ta yi, ya shawarci kungiyar ta Shi’a da ta dauki matakin shigar da kara zuwa kotu ta gaba don kalubalantar hukuncin idan basu gamsu ba.

Dangane da makomar kungiyar ta Shi'a, Farfesan yace muddin gwamnatin Najeriya ta buga hukuncin amincewar kotu na haramta ta a mujalla ta kasa da ake kira da Gazette to fa kungiya ta haramta din din din kamar yadda hakan ta faru ga IPOB mai fafutukar ballewar yankin kabilar Igbo daga Najeriya don kafa kasar Biafra.

Sai dai masanin shari'ar ya jaddada cewa kungiyar ta Yan Uwa Musulmi IMN na da damar kalubantar matakin haramta ta a gaban kotu.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraron cikakken bayanin Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan matsayin Shari'a dangane da matakin haramta ayyukan kungiyar Shi'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.