Isa ga babban shafi
Najeriya

Matakin rufe iyakoki yayi kyakkyawan tasiri kan tattalin arziki - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da matakin gwamnatinsa na wucin gadi kan rufe kan iyakokin kasar na kasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawa da wata tawagar kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, da kuma manoma a Abuja, inda ya ce a halin da ake ciki tattalin arzikin Najeriya ya soma amfana da matakin rufe iyakokin, don yakar matsalar shigar da kayayyaki cikin kasar ta hanyar fasakauri.

A baya bayan nan dai kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ECOWAS, ta shawarci gwamnatin Najeriya ta janye matakin na rufe kan iyakokinta, saboda illar da matakin zai yiwa shirin yankin na yammacin nahiyar ta Afrika, na gudanar da tsarin hada-hadar kasuwancin bai daya.

Sai dai shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa na nan kan bakanta na goyon bayan tsarin kasuwancin bai daya tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS, da kuma nahiyar Afrika baki daya, yarjejeniyar da ya sanyawa hannu a watannin baya. Sai dai shugaban ya ce tilas a gudanar da tsarin kasuwancin na bai daya, bisa tsarin doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.