Kaduna: Yan sanda sun kubutarda daruruwan mutane daga ukuba
Rundunar 'Yan Sandan jihar Kaduna a tarayyar Najeriya ta samu nasarar ceto wasu mutane kimanin 300 da suka hada da manya da kananan yara, da ake tsare da su a wata makaranta dake unguwar Rigasa, da sunan koyar da tarbiya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rundunar ‘yan sandan ta ce ta kai samamen ne bayan samun rahoton zarge-zarge kan makarantar kan batutuwan da suka shafi azabtarwa da kuma yin lalata da yara maza.
Kakakin ‘yan sandan Yakubu Sabo, ya ce daga cikin wadanda suka ceto akwai kananan yara guda 100 da shekarunsu basu fi tara ba, cikin mari, makare a wani karamin daki a ginin makarantar, da sunan basu tarbiya.
Sai dai shugaban makarantar Malam Isma’il ya musanta zarge-zargen da ake yi wa makarantar.
Wakilinmu a Kaduna, Aminu Sani Sado ya aiko mana rahoto kan wannan al’amari.
Kuna iya latsa alamar sautin dake kasa domin sauraron cikakken rahoton.
Yan sanda sun bankado wata makaranta da ake cin zarafin dalibai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu