Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga a Zamfara

Rundunar sojin Najeriya tace dakarunta sun halaka ‘yan bindiga 60 a Zamfara, ciki har da madugunsu da ya shahara, wanda aka fi sani da 'Emir'.

Wasu sojojin Najeriya.
Wasu sojojin Najeriya. AP/Lekan Oyekanmi
Talla

Mukaddashin jami’in yada labaran rundunar Operation Hadarin Daji dake yakar ‘yan bindigar, Captain Ayobami Oni-Orisan, yace, a ranar 3 ga watan Oktoban da muke ciki, dakarun suka halaka yan bindigar 19, bayan da suka afkawa sojojin a SUNKE dake karamar hukumar ANKA, ba tare da an tsokane su ba, duk da wanzuwar shirin cimma sulhu tsakaninsu da gwamnati.

Captain Oni-Orisan yace sojojin sun kuma halaka Karin ‘yan bindiga 39, a ranakun 6 da kuma 7 ga watan Oktoba, yayin samamen da suka kaiwa sansanoninsu dake dazukan Gubarawa da Bawa Daji, inda suka kwato shanu 400.

A ranar Juma’ar data gabata, kwamitin da gwamnan Zamfara ya kafa domin gudanar da bincike kan masu hannu cikin hare-haren ‘yan bindiga da kuma barnar da matsalar ta tafka, ya gano wasu bata-garin jami’an ‘sojoji da yan sanda da kuma sarakunan gargajiya dake assasa matsalar.

Kwamitin dake karkashin jagorancin tsohon sifeta Janar na Yan Sandan Najeriya, Muhammad Abubakar ya gano cewar akwai wasu sarakuna 5 gami da dagatai da masu unguwanni sama da 40 dake taimakawa ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara, sai kuma jami’an soji 10, da yan sanda da kuma wasu ma’aikatan gwamnati.

kwamitin ya ce daga watan Yuni na shekarar 2011 zuwa watan Mayu na 2019 da muke ciki, yan bindiga sun karbi kudin fansar mutanen da suka sace da adadinsa ya zarta naira biliyan 3, daga sama da mutane dubu 3 da 600.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.