Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta haramta fita da shigar hajoji ta kan dukkan iyakokin kasa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da haramci kan shiga da fitar hajoji ta iyakar kasa a fadin kasar a kokarinta na fadada aikin sintirin da ke gudana a a halin yanzu, wadda aka wa lakabi da ‘Exercise Swift Response’.

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

An dai fara wannan aikin sintirin ne a ranar 20 ga watan Agustan shekarar nan da muke ciki, aikin da ya kunshi jami’en kwastan, hukumar shige- da- fice da goyon bayan soji, da sauran hukumomin tsaro.

Ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa ne ke tafiyar da wannan sintiri wanda ya shafi dukkan yankunan kasar har da kudu- maso – kudu, kudu - maso – yamma, tsakiyar varewa da arewa maso – yamma.

A jawabin da ya yi ga manema labarai a Abuja, shugaban kwastan a Najeriya Kanar Hameed Ali ya ce daga yanzu babu wani abin daza a shigar ko a fitar takan iyakokin kasa na kasa, yana mai cewa wannan bai shafi shige da ficen mutane ba.

Da aka tambayeshi ko yaushe ne za a kammala wannan sintiri tare da bude kan iyakokin, Ali ya ce ba za a sassauta ba har sai makwaftan Najeriya sun mika bukatar hawa teburin tattaunawa.

Shugaban kwastan din ya shawarci ‘yan kasuwa da ke shigowa ko fita da hajoji da su yi amfani da tashoshin jiragen ruwa na kasar, tun da sune kawai zabin da suke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.