Isa ga babban shafi
Najeriya

APC ta lashe zaben Bayelsa, na Kogi kuma bai kammalu ba

Hukumar Zaben Najeriya ta bayyana ‘dan takaran gwamnan Jam’iyyar APC a Jihar Bayelsa, David Lyon a matsayin wanda ya samu nasara, sakamakon samun kuri’u 352,552, yayin da abokin takarar sa na PDP Duoye Diri ya samu kuri’u 143,172.

Takardar kada kuri'a a Najeriya.
Takardar kada kuri'a a Najeriya. Reuters
Talla

Mataimakin shugaban Jami’ar Benin, Faraday Orumwese ya sanar da sakamakon.

‘Yan takara 45 ne suka fafata a zaben kujerar gwamnan jihar ta Bayelsa, inda Seriake Dickson ya kammala wa'adinsa.

Yau litinin kuma ake sa ran hukumar zaben Najeriyar ta bayyana wanda ya samu nasara a zaben gwamnan Jihar Kogi. Sai dai a zaben kujerar Sanatan Kogi ta ta yamma, hukumar zaben INEC ta bayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba, wato “Inconclusive”

Rahotannin tashin hankalin da satar akwatunan zabe da kuma kai hari kan masu kada kuri’u sun mamaye zaben.

Sai dai rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta hannun kakakinta Franka Mba, ta musanta gazawa wajen tabbatar da doka da oda yayin zabukan jihohin biyu, inda tace ta iyaka bakin kokarinta wajen samar da tsaro.

Ita kuwa hukumar zaben Najeriya INEC cikin wata sanarwa data fitar, ta ce mafi akasarin wadanda suka cancanta sun kada kuri’unsu yayin zabukan kujerun gwamnan a jihohin na Kogi da Bayelsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.