Saboda akidar addini ake tuhumar El-Zakzaky- Shi'a
Kungiyar Shi’a a Najeriya ta ce, gwamnatin kasar na tuhumar jagoranta ne, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky saboda akidarsa ta addini, amma ba don ya aikata laifuka ba.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta bayyana El-Zakzaky a matsayin fursunan imani, tana mai musanta ikirarin Ministan Yada Labarai na Najeriya, Lai Mohammed da ke cewa, ana tuhumar malamin ne saboda zargin aikata manyan laifuka a kasar .
Ministan ya fadi haka ne a yayin mayar da martani kan rahoton da ke bayyana Najeriya da Comoros da Rasha da Uzbekistan da Cuba da Nicaragua da Sudan a matsayin kasashen da ke keta ‘yancin gudanar da addini.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce, an sanya Najeriya cikin Kudin Bin-Diddigi saboda yadda take cin zarafin wasu mutane masu saboda akidarsa ta addini.
Mai magana da yawun Kungiyar Shi’a a Najeriya, Ibrahim Musa, ya ce, ya dace a dauki mataki kan hukumomin gwamnatin Muhammadu Buhari bisa aika kisan gilla.
Kungiyar Shi’a na zargin sojojin a Najeriya da kashe mata dubban mabiya tare da binne su a katafaren kabarin bai-daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu