Isa ga babban shafi
Najeriya-Kano

Kano ta fuskanci sanyin daya dara na London

Hukumar da ke hasashen yanayi a Najeriya NIMET ta yi gargadin iya ci gaba da fuskantar yanayin tsananin sanyi a Birnin Kano na arewacin kasar dai dai lokacin da binciken hukumar ya nuna sanyi da jihar ta fuskanta a ranaku biyu da suka gabata ya dara wanda birnin London na Birtaniya ya fuskanta.

Yanayin Sanyi a Kano da ke arewacin Najeriya.
Yanayin Sanyi a Kano da ke arewacin Najeriya. News Agency of Nigeria (NAN)
Talla

A cewar hukumar NIMET kamar yadda wasu jaridun Najeriyar suka ruwaito, Kano ta fuskanci sanyi a mataki 8 kan ma’aunin yanayi na Celsius tsakanin ranakun Laraba, Alhamis da kuma yau Juma’a yayinda Birtaniya ta fuskanci mataki 11 ga ma’aunin.

Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama ne suka kauracewa fita waje a ranakun ciki har da yau Juma’a, dai dai lokacin kakkarfar iska ke ci gaba da kadawa.

A hasashen NIMET, ta bayyana cewa sanyin da iska mai dauke da kura zai ci gaba da karade jihohin arewacin Najeriyar musamman wadanda suka hada iyaka da Jamhuriyyar Nijar ciki har da Kano Katsina Sokoto da Zamfara da kuma garuruwan da ke da tekuna ko kuma gab da tekunan.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa ba lallai jihohin da ke tsakiyar Najeriya su fuskanci makamancin zafin na Kano ba, yayinda Jihohin Adamawa da Gombe da Bauchi da Kaduna da kuma Pulato za su fuskanci matsakaicin sanyi daga maki 10 zuwa 36 kan ma’aunin yanayi na Celsius.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.